HAKURI

“Abin mamaki ga al’amarin mumini, lallai al’amarin sa dukkan shi alkhairi ne, babu me samun haka fa ce mumini, idan farin ciki ya same shi sai yayi godiya ga Allah, sai abin ya kasance alkhairi gare shi, idan cuta ta same shi sai ya yi haƙuri sai haƙurin ya kasance alkhairi agare shi.” [Muslim].

Nana Aisha (R.A)

كان اجود الناس وكان اجود ما يكون في رمضان فلرسول الله صلى الله عليه وسلم اجود باالخير من الريح المرسلة

Manzon Allah (SAW) yafi kowa karamci, kuma yafi karamci a cikin Watan Ramadan, kuma lallai Manzon Allah (SAW) yafi karamci da Alkhairi sama da iska mai ratsawa (ratsa jiki). [Bukhari da Musulim].

Manzon Allah (SAW)

Yace: "Babu wani Musulmi da zai yiwa ɗan uwan sa addu'a a bayan idon sa, face Mala'ika yace: Kaima Allah baka". (Muslim ya ruwaito)

Daga Sahl bn Sa'ad

"Manzon Allah (SAW) Yace:

"Allah Yana da taskokin Alkhairi da na sharri, mutane su ne mabuɗansu, Madallah da bawan da ya zamo mabuɗin alkhairi makullin sharri, Tir da bawan da ya zamo mabuɗin sharri makullin Alkhairi".

Manzon Allah ﷺ

Ya ce :

"Idan Zina da cin Riba suka bayyana a cikin wata alqarya, to mutanen garin sun saukarwa kansu da kansu Azabar Allah."

Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama

Yace:

"Na haneku da zato, domin shi mafi ƙaryar zance ne.

Wannan bawai yana hana yin zato bane, amma dai yana hani da yawan yin mummunan zato, domin wani lokacin yakan zo da ƙarya acikinsa"

Manzon Allah ﷺ

Ya ce:

"Wanda Allah ya azurtashi da mace ta gari to hakika Allah ya taimakeshi a kan rabin addininsa, to ya ji tsoron Allah a sauran rabin".

Shaykhul Islami Ibnu Taimiya(RA) ya ce: "Soyayya da rahama suna kasancewa daga wajenta, (Mace ta gari) abin da Allah ya yi mata baiwarsa"

Daga Albaraa' Bn Aazib (RA)

Manzon Allah (SAW) yace min: Idan ka zo kwanciya barci, to ka yi alwala irin alwalarka ta sallah, sannan ka kwanta ta 6arinka na daama, kuma ka ce:

""اللَّهُمَّ أَسْلَمْتُ نفِسي إِلَيكَ، وَفَوَّضتُ أَمري إِلَيْكَ، وَأَلَجَأْتُ ظَهرِي إِلَيْكَ، رغبةً ورهْبَةً إِلَيْكَ، لامَلجأَ ولا مَنجى مِنْكَ إِلاَّ إِليكَ، آمنتُ بِكِتَابِكَ الذِي أَنزَلْت، وَبِنَبِيِّكَ الذِي أَرسَلتَ"".

DAGA FARIN JAKADA

"Manzon Allah (SAW) Yace: ""Masu Tuba Daga Zunubi, Kamar Basu yi Zunubi bane""

TUBA GA ALLAH

"Manzon Allah (s.a.w) yace:

Yaku mutane ku tuba zuwa ga Allah, hakika ni ina tuba zuwa gareshi a rana sau dari."

Manzon Allah (SAW)

Yace:

""Mafi kusancin lokacin da bawa ke kasancewa kusa da ubangijinsa shine Lokacin sujada, ku yawaita addu'a a yayin sujjada" [Muslim ne ya ruwaitoshi].

Annabi (ﷺ)

Yace:

"Lallai tausasawa ba'a samunta acikin wani Abu face ta kawatashi, Kuma ba'a cire ta daga komai face ta tozarta shi" Muslim ne ya ruwaitoshi.

Manzon Allah (s.a.w)

Yace:

"Yaku mutane ku tuba zuwa ga Allah, hakika ni ina tuba zuwa gareshi a rana sau dari."

Manzon Allah (SAW)

Ya ce: ""Ba ya halatta ga musulmi ya kaurace ma dan uwansa sama da kwanaki uku ba, Su na haduwa sai wannan ya dauke kansa, wancan ma ya dauke kansa, Amma mafi alkhairi daga cikinsu shine wanda ya fara yi ma dan uwansa sallama"". Bukhariy da Muslim