INGANTACCEN ZIKIRI:
اَللّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اَللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارِكْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ.” t";
Manzon Allah SAW ya ce:
:"Ku yawaita salati a gareni a daren Juma'a da ranar Juma'a, wanda yayi salati daya a gareni, Allah zai yi salati goma a gareshi"" Baihaqiy, Albaniy ya ingantashi"
Shaykh Ibn Al-Usaimeen (RH)
Yace: “Ranar Juma’a rana ce ta Taruwa, a na kiranta da haka ne saboda Allah ya tara al'amuran halittan duniya da na shari’a a cikinta, wanda babu ranar da ta hada hakan sai ita.
Salati ga Manzon
Wanda ya lizimci yawaita salati ga Manzon Allah damuwanshi da bakinciki za su kwaranye
Salati ga Manzon Allah
AWanda ya lizimci yawaita salati ga Manzon Allah damuwanshi da bakinciki za su kwaranye, Musamman a ranar Juma'a.
Ibnul Qayyim Allah yayi masa rahama ya ce:
Zikiri shi ne kofar Allah mafi girma kuma budadde a tsakaninsa da bawansa muddin bawan bai kulle kofar da gafalarsa ba.
Ibnul Qayyim Rahimahullah
Yana cewa: "Ranar juma'a rana ce ta ibada, matsayinta a cikin ranaku tamkar matsayin watan Ramadan ne a cikin watanni, lokacin karbar addu'ar da ke cikinta kuma tamkar daren lailatul qadri ne da yake cikin watan Ramadan"".