𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
:
Malam, mene ne hukuncin mutumin da ba ya ɗaukar nauyin ’ya’yansa tun suna kanana?
:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
:
To, ai da ma irin wannan shi ne kuskuren da mutane su ke yi; su yi ta haihuwa alhali ba su da wadatar da za su iya ɗaukar nauyin ’ya’yan. Sai kuma a wayi gari su na cewa ‘ai Annabi ya na son a hayayyafa da yawa’. Ba haka Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya ke nufi ba. Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya na nufin a haihu a rike hakkin yaran. Idan ba za ka iya rike hakkinsu ba, to ka haihu daya-biyu-uku ka hakura. Wajibi ne a kan iyaye su rike hakkin nauyin ’ya’yansu, amma duk mutumin da ya san ba zai iya rike hakkin ’ya’yansa ba, to ya daina haihuwa. Da yawa mutane su na zaluntar al’ummar, suna zaluntar ’ya’yansu; su yi ’ya’ya da yawan da ba su da ikon da za su rikesu su kula da su ba, idan an yi mu su magana su ce ‘ai Allah Ne Ya ke da arziki a hannu’.
Wannan kuskure ne. Ko kuma su mata su rika gasar haihuwa, alhali ba sa iya kula da ’ya’yan ko lafiyarsu. Wannan kuskure ne kuma jahiltar fahimtar addini ne da hadisan Annabi Sallallahu alaihi Wasallam. Wajibi ne a kan iyaye su ɗauki nauyin ’ya’yansu. Amma idan har iyaye su ka yi sakaci da ganganci ba su ɗauki nauyin ’ya’yansu ba, to wajibin hukuma ne ta ɗauki nauyin Waɗannan yara. Idan hukuma ta yi sakaci, to wajibin ragowar al’umma ne su ɗauki nauyinsu. Shi ya sa a ke son a rika kafa sahihiyar gwamnati mai aiki da koyarwar Shari’ar Musulunci. Allah ya bamu irinta ameen.
WALLAHU A’ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu…
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ