Uncategorized

KADA KUYI GULMA.

Daga

Muhammad Umar Baballe.
Abu Amatillah.

Wani yana nan yana gararanbarsa a gari, duk inda kuka zauna ku kuma sai kun zageshi. Wannan iskancin da yakeyi haka za azo a raba muku. To tunda kunyi gulmarsa, zai wuce haka ne, za a cire masa haƙƙinsa ko baza a cire masa ba?, za a cire masa. Idan kaga mutum akan hanyar da ta kauce kayi masa gyara, kayi masa nasiha”

 

Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum.

 

“Duk wanda kaka yana aikata wani abu ba daidai ba, to ba guri za ka samu ka zauna kaita yin gulmarsa ba, ka kirashi gefe guda kayi masa nasiha ka nusar dashi kuskurensa domin ya gyara”

 

“Amma matuƙar ka koma gefe kana zaginsa kana aibanta shi a bisa kuskuren da yake yi, to haƙiƙa da sannu za ka rage masa yawan tarin zunuban da suke a kansa a dalilin gulmarsa da kakeyi kana zaginsa”

 

Allah ta’ala yasa mu dace baki ɗaya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *