Allah Buwayi

Gagara misali Yace:
"وَإِنِّي لَغَفَّارٌ لِّمَن تَابَ وَآمَنَ وَعَمِلَ صَالِحًا ثُمَّ اهْتَدَىٰ" (طـه :82) ""Kuma lalle Nĩ haƙĩƙa Mai gãfara ne ga wanda ya tũba kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, sa'an nan kuma ya nẽmi shiryuwa".

MUTUWA

Allah Buwayi Gagara Misali Yace:
أَيْنَمَا تَكُونُوا يُدْرِكْكُمُ الْمَوْتُ وَلَوْ كُنْتُمْ فِي بُرُوجٍ مُشَيَّدَةٍ ۗ وَإِنْ تُصِبْهُمْ حَسَنَةٌ يَقُولُوا هَٰذِهِ مِنْ عِنْدِ اللَّهِ ۖ "Inda duk kuka kasance, mutuwa zã ta riske ku, kuma kõ da kun kasance ne a cikin gãnuwõyi ingãtattu!".

Ibnul Qayyim Rahimahullah

Ibnul Qayyim Rahimahullah ya ce: "ALƘUR'ANI waraka ne ga abin da ya ke zuciya, ya na tafiyar da abin da Shaydan ke jefawa a cikin zuciya na daga wasu-wasi, sha'awoyi da munanan nufi lalatattu

Allah

Subhanahu Wa taala- Yana cewa:
وَلَا ‌تَقۡفُ مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٌۚ إِنَّ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡبَصَرَ وَٱلۡفُؤَادَ كُلُّ أُوْلَٰٓئِكَ كَانَ عَنۡهُ مَسۡـُٔولٗا ) [الإسراء: 36] Ma’ana: “Kuma kada ka bi abin da bã ka da ilmi game da shi. Lalle ne jĩ da gani da zũciya, dukan waɗancan (mutum) yã kasance daga gare shi wanda ake tambaya.”

*Ginshiƙan zuciya*

basa ƙarfafa sai da Alqur'ani, idan har mutum ya bar karanta Alqur'ani to lallai za suyi rauni

*Alqur'ani*

Duk yadda mutum zai samu magani mai gusar da damuwa ba zai samu Kamar Alqur'ani ba

Ibnul~qayyim (Rh) Yace

:"Ma'abota Al-Qur'ani sune masu koyansa kuma masu aiki da abunda ke cikinsa koda kuwa basu samu daman haddaceshi a haƙiƙanin cikin zuƙatansu ba, amma wanda ya haddaceshi bai fahimceshi ba kuma bai yi aiki da abunda ke cikinsa ba to tabbas baya daga cikin ma'abota shi Al-Qur'anin koda ya kasance yana jera haruffan kamar yadda ake jera kibbau a cikin kwarinsu."