Uncategorized

HUKUNCIN CIN YANKAN ARNA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
:
Assalamu alaikum,Allah ya qarawa mallam Ameen, tambaya na anan shine shin Mallam zamu iya cin yankan arna? waɗanda ba musulmai ba?
:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
:
EH ya halatta muci yankan da Kirista ko Yahudawa suka yanka. Amma da sharadi kamar haka:

1. Ya zamto yankan basu yishi domin wanin Allah ba. Saboda faɗin Allah (swt):

حُرِّمَتْ عَلَيْكُمُ الْمَيْتَةُ وَالدَّمُ وَلَحْمُ الْخِنْزِيرِ وَمَا أُهِلَّ لِغَيْرِ اللَّهِ بِهِ وَالْمُنْخَنِقَةُ وَالْمَوْقُوذَةُ وَالْمُتَرَدِّيَةُ وَالنَّطِيحَةُ وَمَا أَكَلَ السَّبُعُ إِلَّا مَا ذَكَّيْتُمْ وَمَا ذُبِحَ عَلَى النُّصُبِ وَأَنْ تَسْتَقْسِمُوا بِالْأَزْلَامِ ۚ ذَٰلِكُمْ فِسْقٌ ۗ الْيَوْمَ يَئِسَ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ دِينِكُمْ فَلَا تَخْشَوْهُمْ وَاخْشَوْنِ ۚ الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا ۚ فَمَنِ اضْطُرَّ فِي مَخْمَصَةٍ غَيْرَ مُتَجَانِفٍ لِإِثْمٍ ۙ فَإِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَحِيمٌ
An haramta muku mũshe da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah a gare shi, da mãƙararriya da jefaffiya da mai gangarõwa da sõkakkiya, da abin da mãsu dãgi suka ci, fãce abin da kuka yanka, da abin da aka yanka a kan gunki (shĩ ma an haramta). Kuma kada ku yi rabo da kibiyoyi na cãca wannan fãsiƙanci ne. A yau waɗanda suka kãfirta sun yanke ƙauna daga addininku. Sabõda haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõroNa. A yau Nã kammalã muku addininku, Kuma Nã cika ni´imaTa a kanku, Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku. To, wanda aka sanya wa lalũra a cikin yunwa mai tsanani, bã yana mai karkata zuwa ga wani zunubi ba, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. (suratul Ma’idah aya ta 3).

2. Ya zamto sunan Allah suka ambata yayin da zasu yanka dabbar. Idan suka yanka da Sunan Jesus ko Holy spirit ko sunan wani pastor, to ba za’a ci ba. Allah (swt) yana cewa:

وَلَا تَأْكُلُوا مِمَّا لَمْ يُذْكَرِ اسْمُ اللَّهِ عَلَيْهِ
Kada ku ci daga abin da ba a ambaci sũnan Allah ba a kansa. (suratul An’am ayah ta 121).

3. Ya kasance abinda suka yanka ɗin baya daga cikin irin dabbobin da Allah ya haramta mana. Misali, alade ko kare ko jaki ba zai halatta aci ba koda sun yanka shi tare da ambaton sunan Allah.

Amma bai halatta musulmi yaci abinda ‘yan addinin Buddah ko hindu suka yanka ba. Koda sun ambaci sunan Allah yayin da zasu yanka dabbar.

WALLAHU A’ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu…
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *