Ibnul~qayyim (Rh)

Yace: "Ma'abota Al-Qur'ani sune masu koyansa kuma masu aiki da abunda ke cikinsa koda kuwa basu samu daman haddaceshi a haƙiƙanin cikin zuƙatansu ba, amma wanda ya haddaceshi bai fahimceshi ba kuma bai yi aiki da abunda ke cikinsa ba to tabbas baya daga cikin ma'abota shi Al-Qur'anin koda ya kasance yana jera haruffan kamar yadda ake jera kibbau a cikin kwarinsu."

*Ginshiƙan zuciya*

basa ƙarfafa sai da Alqur'ani, idan har mutum ya bar karanta Alqur'ani to lallai za suyi rauni

*Alqur'ani*

Duk yadda mutum zai samu magani mai gusar da damuwa ba zai samu Kamar Alqur'ani ba

Shaykh Ibnu Baaz(Rahimahullah)

Ya ce:

""Akwai alkhairi mai yawa a cikin yawaita sallar Nafila, Domin Allah yana cike tawayar sallar farillah dashi tare da samun ladaddaki masu girma"".

Hadith from Bukhari and Muslim

Lallai a Aljannah akwai wata kofa da a ke ce mata Arrayyan, a ranar Alkiyama masu azumi za su shiga ta wannan kofar, babu wanda zai Shiga ta cikin ta face su, idan kuma suka shiga sai a kulle, babu wanda zai sake shiga ta cikin ta"". Bukhary da Muslim"