Hakuri

“Abin mamaki ga al’amarin mumini, lallai al’amarin sa dukkan shi alkhairi ne, babu me samun haka fa ce mumini, idan farin ciki ya same shi sai yayi godiya ga Allah, sai abin ya kasance alkhairi gare shi, idan cuta ta same shi sai ya yi haƙuri sai haƙurin ya kasance alkhairi agare shi.” [Muslim].

Hakuri

Imamu Ahmad yana cewa: “Haƙuri a cikin jikin ɗan Adam yana da matsayi kamar kai ne, kuma duk mutumin da ba shi da kai to gangar jikinsa ma ba tada amfani.”

Hakuri

Haske ne mai haskaka zuciya sai dai hasken tafe yake da zafi wanda sai bawa ya jure. Haƙuri ya fi dutse nauyi a zuciyar bawa kuma ya fi maɗaci ɗaci a zuciya sai dai amma ya fi zuma zaƙi da daɗaɗa rai wurin sakamako.

Ibnul Qayyim (رحمه الله)yace:

Ibnul Qayyim (رحمه الله)yace: "Mafi sani daga cikin masana, shine wanda yakai karan ransa zuwa ga Allah".

Babu

:ani mai rubutu face sai ya gushe. Abin da kuma ya rubuta da hannunsa ya wanzu tsawan lokaci. Kada ka rubuta wani abu da tafin hannunka. Face abin da zai faranta maka rai ka ganshi ranar Alƙiyama.

Imam Azzahaby

yana cewa: "Idan Fitintinu suka afku, to ka yi riqo da Sunnah, Kuma ka kame bakin ka, kar da ka kutsa cikin abin da babu ruwan ka, duk abin da ya shige maka duhu to ka mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa(Me Allah da Manzonsa suka ce), ka tsaya(kar ka ce komai) ka ce: Allah ne Mafi Sani(Allahu a'lam)

Shaykhl Islam Ibn Taimiyyah (RA)

Ya ce: Misalin 'yan uwantaka saboda Allah, kamar misalin hannu da ido ne, idan ido ya zubar da hawaye sai hannu ya share masa, idan kuma hannu ya ji ciwo sai idon ya zub da hawaye sabo da zafin da hannu ya ke ji.

Haƙiƙa

shi ilmin addini shine ado da kwalliya a garemu, dukkanin wanda bashida ilmin addininsa, to haƙiƙa yana cikin duhun jahilci wanda shaiɗan ya dilmiya shi cikinsa

Imanin ka

Duk abinda ka rasa, matuƙar imanin ka na tare da kai wallahi ba ka yi hasara ba, duk abinda za ka samu kuma, matuƙar ka rabu da imanin ka wallahi ka yi hasarar duniya da lahira

Babbar hanya

Babbar hanyar gyara shi ne faɗin laifukan mutum gare shi, domin shine da alhakin gyara su, amma faɗin su ga wanin sa ba zai canza komai ba

Abu mafi kyau

Abu mafi kyau shine mutum ya zama cikin masu godiya a lokacin wadata, kuma ya zama cikin masu haƙuri a lokacin jarabta

Sharri da Alkairi

Sharri da Alkairi duk ƴan aike ne, indai ka aika su to za su dawo, sai dai akwai yiyuwar su daɗe. Sai ka kula da wa za ka aika

Hanyoyin guda biyu ne.

Hanyoyin guda biyu ne. Kodai ka tuna Allah ya tuna ka, ko ka manta shi ya manta ka

*Cikakkiyar ƙauna*

*Cikakkiyar ƙauna*Itace ka riƙa roƙa ma wanda kake ƙauna alherin duniya da lahira a gurin Allah, ba tare da ya sani ba

Ka kasance

Ka kasance mai fadar gaskiya koda zata sanya ka kuka da bakin cikin rayuwa

Ka kasance

Ka zamo mai wayo, amma karka yadda ya kaika ga zalunci

Ka kasance

Ka zamo mai kyauta, Amma kar kyauta ta janyo maka riya

Ka zamo

Ka zamo mai hakuri, amma kar ka yadda hakuri ya jawo raini

Ibnul Qayyim Rahimahullah Yace

Bata lokaci ya fi mutuwa muni, domin mutuwa takan raba ku da rayuwar duniya ne, alhali bata lokaci yana raba ku da Allah ne.

LALLAI KA SANI!!!

Haƙiƙa Allah shine mafi tausayin bayinsa, kuma yana saukar da rahamarsa ne ga waɗanda yaso, kuma shi yana kau da kai, yana yafiya a lokacin da ka tuba ka dawo gareshi sannan kuma ka nemi gafararsa, shine kaɗai wanda zai amshi addu'arka a lokacin da ka roƙeshi, yana da hikima acikin dukkanin abinda yayi a gareka.

Al-hafiz Ibn Rajab (Rh) ya ce

Sau da yawa mu'amalantar mutane da magana mai dadi ya fi soyuwa a garesu daga ciyar da su abinci ko kyautata musu ta hanyar ba su kyautan kudi, Kamar yanda Luqmanul hakeem ya fada wa dansa cewa: Yaa kai 'dana: Ya kasance maganarka ta zamto mai dadi, kuma ka zamto mai sakin fuska ga mutane, za ka zama mafi soyuwa a gurin mutane fiye da wanda yake ba su dinari da dirhami.

Ibnul Qayyim (Rahimahullah) yace:

Mafi tsananin uquba a duniya shine Allah ya rike harshenka daga ambatonsa.

AMBATON ALLAH

Ba a taɓa ambaton Allah a kan wani wahala ba face ya sauƙaƙa, ko a kan wani ƙunci face ya sauƙaƙa, ko a kan wani tsanani face ya gushe, ko a kan wani damuwa face (Allah Maɗaukakin Sarki) ya yaye wannan damuwar. (Muhammad Umar Baballe)

Akwai wasu mutane

Akwai mutanen da suke da Kai amma babu mai amfanuwa da wannan kan nasu sai masu aski.

Hasanul Basri (Rahimahullah) Yace:

Lallai mutum ya kanyi magana a lokacin FUSHINSA wadda zata ruguza masa Ayyukansa na shekaru 60 ko shekaru 70"".

Maganin damuwar mu

Muji tsoron Allah: Sai Allah ya warware mana damuwar mu, mu kauce ma saɓonsa, sai yaji ƙanmu, kada mu bari shaiɗan yayi tasiri akanmu ya shiga tsakanin mu da ubangijin mu Allah ya kuma halaka mu ƙarshe mu zamto ababen yin nadama a ranar ƙiyamah.

Koda yaushe:

Muna yin tunani ne akan yawan matsalolin da suke damun mu ne a rayuwa, muna mantawa da cewa lallai fa haƙiƙa Allah yana da mafita daga dukkanin kowace irin matsalar da ta dame mu a rayuwa.

Yawan haƙuri

"""Wasu bazasu goyi bayan ka ba, wasu zasu gujeka, wasu kuma zasu tsaneka, amma babu makawa duk irin hukuncin da mutane zasu yi akanka, tabbas Allah yana mai taimakon ka akansu matuƙar ka riƙi gaskiya da kuma adalci ga bayin Allah, domin shine yasan dukkanin wani juyin lamuranka, kuma shine zai ɗaukar maka fansa akan azzãlumai musamman idan ka kasance mai yawan yin haƙuri, domin lallai Allah yana son masu haƙuri"

Yawan biyayya ga Allah

"Idan ka kasance mai yawan ɗa'a da biyayya ga Allah maɗaukakin sarki, sai ya zamto mai baka kariya daga dukkanin maƙiya ko masu nufinka da sharri ko mummunan lamari akanka, kayi haƙuri da jarabawarsa, ka jure duk wani halin ƙunci da zaka shiga, ka bautawa Allah yadda aka buƙaceka da ita, sai Allah ya baka kyakkyawan matsayi a gurinsa"

Lallai kasani!

Haƙiƙa Allah shine mafi tausayin bayinsa, kuma yana saukar da rahamarsa ne ga waɗanda yaso, kuma shi yana kau da kai, yana yafiya a lokacin da ka tuba ka dawo gareshi sannan kuma ka nemi gafararsa, shine kaɗai wanda zai amshi addu'arka a lokacin da ka roƙeshi, yana da hikima acikin dukkanin abinda yayi a gareka"

Mutane masu daraja

Suke shiga jarrabawa. Don haka, kar ka damu don kana cikin jarrabawa, ka roƙi Allah ya baka ikon cin jarrabawar. (Salis Harun Usman)

Abin mamaki

Ya tabbata ga Wanda yaji tsoron zafin rana a duniya, amma ta yaya ba zai ji tsoron zafin jahannama ba a ranar Alƙiyama ta hanyar nisantar zunubai.

Imãm Shafi'i Rahimahullaah Yace:

Kayi sani cewa bazaka taɓa yardar da dukkanin mutane ba, kai dai kayi ƙoƙarin inganta tsakaninka da Allah maɗaukaki, idan ka daidaita tsakaninka da Ubangijinka kada ka damu da mutane"".

YAN UWANTAKA

Lema ba ta hana saukar ruwan sama amma tana rage saukan ruwan a jiki ko saussauta hakan, idan ba ka iya kawar da matsalar dan uwanka da damuwarsa, to ka zamto masa lema mai rage masa damuwa.""

NAGARI

"""IDAN NAGARI SUKA YI RIKO DA HANNUN MASU BARNA, SAI SU TSIRA BAKI DAYANSU"".

Addinin Musulunci:

Yana kiranmu da barin cutar da juna, kuma kar mu rama cutarwa da cutarwa, saidai mu yi afuwa, mu yi yafiya, mu tunkuɗe cutarwa da alkhairi...

Ibnul Qayyim Allah yayi masa rahama ya ce:

Zikiri shi ne kofar Allah mafi girma kuma budadde a tsakaninsa da bawansa muddin bawan bai kulle kofar da gafalarsa ba.

Annabi (ﷺ) yace:

Lallai tausasawa ba'a samunta acikin wani Abu face ta kawatashi, Kuma ba'a cire ta daga komai face ta tozarta shi" Muslim ne ya ruwaitoshi