Manhajar Kalaman Hikima tana kunshe da bangarori da yawa a cikin ta. Zaka samu dubannin gajerun maganganu da suka hada da hadisai, ayoyin Alqur’ani, Kalaman Hikima daga manyan malaman musulunci da sauran gajerun maganganu na fadakarwa, wa’azantarwa da tunatarwa akan addinin Musulunci. Duk domin dorawa a kafofin sada zumunci na zamani kamar Facebook, WhatsApp, Twitter, Instagram da sauransu.
Manhajar tana da saukin amfani, domin zata nuna maka yanda zakayi amfani da ita a farkon budewa, kuma kaima idan kana da wani abun da kake so ka rubuta a ciki, akwai bangaren da zai baka damar ka rubuta cikin sauki