Sheikhul Islam Ibn Taimiyyah (Rh)
"Shi fa kabari da kake gani mutane basa ganin rana ballantana wata, mutum yana samun haskene sakamakon kasancewarsa cikin masu yin sallah."
Khalid bin Walid (RA)
"Jihadi yaƙe-yaƙe ya shagaltar damu ga barin karanta ka, A yau kuma ko me yake shagaltar damu ga barin karanta shi..."
Ibnul Qayyim (رحمه الله)
"Mafi sani daga cikin masana, shine wanda yakai karan ransa zuwa ga Allah."
Ibnu Taimiyyah (Rahimahullah)
"Mace tana da bukatar kula da tsaro sama da yanda karamin yaro yake da bukata, kuma duk abin da zai zamo ya suturce ta, ya katange ta, shi yafi gurin inganta mata rayuwarta."
Imam Azzahaby
"Idan Fitintinu suka afku, to ka yi riqo da Sunnah, Kuma ka kame bakin ka, kar da ka kutsa cikin abin da babu ruwan ka, duk abin da ya shige maka duhu to ka mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa(Me Allah da Manzonsa suka ce), ka tsaya(kar ka ce komai) ka ce: Allah ne Mafi Sani(Allahu a'lam)"
Shaykhul Islam Ibn Taimiyyah
"Misalin 'yan uwantaka saboda Allah, kamar misalin hannu da ido ne, idan ido ya zubar da hawaye sai hannu ya share masa, idan kuma hannu ya ji ciwo sai idon ya zub da hawaye sabo da zafin da hannu ya ke ji."
Ilmin Addini
"Haƙiƙa shi ilmin addini shine ado da kwalliya a garemu, dukkanin wanda bashida ilmin addininsa, to haƙiƙa yana cikin duhun jahilci wanda shaiɗan ya dilmiya shi cikinsa"
Ibnul Arabiy Rahimahullah
"Mace Tagari ba tana zuwa bane da iya neman mutum, Ita arziki ne na Allah wanda yake bayarwa ga wanda yake tsoronshi."
Al-Muzany (Rahimahullah)
"Kowacce rana da Allah ya halitta tana cewa: 'Ya ɗan adam kayi amfani dani watakila bazaka rayu zuwa wani yinin ba, kowane dare da Allah ya halitta yana cewa: 'Ya ɗan adam kayi amfani dani watakila bazaka ƙara kaiwa wani daren ba'."
Shaykh Ibnu Uthaimeen
"Wanda ya taimaki wani a kan yi wa Allah da'a/biyayya cikin ayyukan da'a ma Allah, to yana da kwatankwacin ladansa ba tare da an rage wani abu daga nashi ladan ba".
Hasanul-Basariy Allah Rahimahullah
"Ana bijirowa da ɗan adam hoton rayuwarsa ta duniya a ranar ƙiyamah, dukkanin wani lokacin da ya wuce shi ba tareda ya aikata wani abin alkhairi ba, sai yaji zuciyarsa tamkar zata kekkece sabida nadama"
Malik bn Dinar (Rahimahullah)
"Yazo garemu cewa za'a ce da mai yawan bautawa Allah shiga Aljanna, za kuma ace da Malami tsaya kayi ceto"
Ibnul Qayyim Rahimahullah
"Bata lokaci ya fi mutuwa muni, domin mutuwa takan raba ku da rayuwar duniya ne, alhali bata lokaci yana raba ku da Allah ne."
Ibnul Qayyim Rahimahullah
"ALƘUR'ANI waraka ne ga abin da ya ke zuciya, ya na tafiyar da abin da Shaydan ke jefawa a cikin zuciya na daga wasu-wasi, sha'awoyi da munanan nufi lalatattu".
LALLAI KA SANI!!!
Haƙiƙa Allah shine mafi tausayin bayinsa, kuma yana saukar da rahamarsa ne ga waɗanda yaso, kuma shi yana kau da kai, yana yafiya a lokacin da ka tuba ka dawo gareshi sannan kuma ka nemi gafararsa, shine kaɗai wanda zai amshi addu'arka a lokacin da ka roƙeshi, yana da hikima acikin dukkanin abinda yayi a gareka.
Shaykh Ibnu Baaz(Rahimahullah) ya ce:
"Akwai alkhairi mai yawa a cikin yawaita sallar Nafila, Domin Allah yana cike tawayar sallar farillah dashi tare da samun ladaddaki masu girma".
Al-hafiz Ibn Rajab (Rh) ya ce:
Sau da yawa mu'amalantar mutane da magana mai dadi ya fi soyuwa a garesu daga ciyar da su abinci ko kyautata musu ta hanyar ba su kyautan kudi, Kamar yanda Luqmanul hakeem ya fada wa dansa cewa: Yaa kai 'dana: Ya kasance maganarka ta zamto mai dadi, kuma ka zamto mai sakin fuska ga mutane, za ka zama mafi soyuwa a gurin mutane fiye da wanda yake ba su dinari da dirhami.
Lallai kasani!
Haƙiƙa Allah shine mafi tausayin bayinsa, kuma yana saukar da rahamarsa ne ga waɗanda yaso, kuma shi yana kau da kai, yana yafiya a lokacin da ka tuba ka dawo gareshi sannan kuma ka nemi gafararsa, shine kaɗai wanda zai amshi addu'arka a lokacin da ka roƙeshi, yana da hikima acikin dukkanin abinda yayi a gareka.