Manzon Allah (SAW) ya ce:

Manzon Allah (SAW) ya ce: ""Ba ya halatta ga musulmi ya kaurace ma dan uwansa sama da kwanaki uku ba, Su na haduwa sai wannan ya dauke kansa, wancan ma ya dauke kansa, Amma mafi alkhairi daga cikinsu shine wanda ya fara yi ma dan uwansa sallama"". Bukhariy da Muslim"

Manzon Allah (SAW) ya ce:

“Babu cuta babu cutarwa”. Hadisine Hasan, Ibnu Majah da Daraƙuɗuniy suka ruwaito shi.

Lallai kasani!

Haƙiƙa Allah shine mafi tausayin bayinsa, kuma yana saukar da rahamarsa ne ga waɗanda yaso, kuma shi yana kau da kai, yana yafiya a lokacin da ka tuba ka dawo gareshi sannan kuma ka nemi gafararsa, shine kaɗai wanda zai amshi addu'arka a lokacin da ka roƙeshi, yana da hikima acikin dukkanin abinda yayi a gareka"

Yawan biyayya ga Allah

"Idan ka kasance mai yawan ɗa'a da biyayya ga Allah maɗaukakin sarki, sai ya zamto mai baka kariya daga dukkanin maƙiya ko masu nufinka da sharri ko mummunan lamari akanka, kayi haƙuri da jarabawarsa, ka jure duk wani halin ƙunci da zaka shiga, ka bautawa Allah yadda aka buƙaceka da ita, sai Allah ya baka kyakkyawan matsayi a gurinsa"

Yawan haƙuri

"""Wasu bazasu goyi bayan ka ba, wasu zasu gujeka, wasu kuma zasu tsaneka, amma babu makawa duk irin hukuncin da mutane zasu yi akanka, tabbas Allah yana mai taimakon ka akansu matuƙar ka riƙi gaskiya da kuma adalci ga bayin Allah, domin shine yasan dukkanin wani juyin lamuranka, kuma shine zai ɗaukar maka fansa akan azzãlumai musamman idan ka kasance mai yawan yin haƙuri, domin lallai Allah yana son masu haƙuri"

Koda yaushe:

Muna yin tunani ne akan yawan matsalolin da suke damun mu ne a rayuwa, muna mantawa da cewa lallai fa haƙiƙa Allah yana da mafita daga dukkanin kowace irin matsalar da ta dame mu a rayuwa.

Maganin damuwar mu

Muji tsoron Allah: Sai Allah ya warware mana damuwar mu, mu kauce ma saɓonsa, sai yaji ƙanmu, kada mu bari shaiɗan yayi tasiri akanmu ya shiga tsakanin mu da ubangijin mu Allah ya kuma halaka mu ƙarshe mu zamto ababen yin nadama a ranar ƙiyamah.

Hasanul Basri (Rahimahullah) Yace:

Lallai mutum ya kanyi magana a lokacin FUSHINSA wadda zata ruguza masa Ayyukansa na shekaru 60 ko shekaru 70"".

Akwai wasu mutane

Akwai mutanen da suke da Kai amma babu mai amfanuwa da wannan kan nasu sai masu aski.

Tausasawa

Annabi (ﷺ) yace: Lallai tausasawa ba'a samunta acikin wani Abu face ta kawatashi, Kuma ba'a cire ta daga komai face ta tozarta shi" Muslim ne ya ruwaitoshi

Manzon Allah:

Sallallahu alaihi wasallama yace: Na haneku da zato, domin shi mafi ƙaryar zance ne. "Wannan bawai yana hana yin zato bane, amma dai yana hani da yawan yin mummunan zato, domin wani lokacin yakan zo da ƙarya acikinsa"

Al-hafiz Ibn Rajab (Rh) ya ce

Sau da yawa mu'amalantar mutane da magana mai dadi ya fi soyuwa a garesu daga ciyar da su abinci ko kyautata musu ta hanyar ba su kyautan kudi, Kamar yanda Luqmanul hakeem ya fada wa dansa cewa: Yaa kai 'dana: Ya kasance maganarka ta zamto mai dadi, kuma ka zamto mai sakin fuska ga mutane, za ka zama mafi soyuwa a gurin mutane fiye da wanda yake ba su dinari da dirhami.

Soyayya don Allah

Ka zamo mai soyayya don Allah, amma kada ka cutar da wanda yake sonka don Allah

Ibnul Qayyim Rahimahullah Yace

Bata lokaci ya fi mutuwa muni, domin mutuwa takan raba ku da rayuwar duniya ne, alhali bata lokaci yana raba ku da Allah ne.

Ka zamo

Ka zamo mai hakuri, amma kar ka yadda hakuri ya jawo raini

Ka kasance

Ka zamo mai kyauta, Amma kar kyauta ta janyo maka riya

Ka kasance

Ka zamo mai wayo, amma karka yadda ya kaika ga zalunci

Ka kasance

Ka kasance mai fadar gaskiya koda zata sanya ka kuka da bakin cikin rayuwa

Wanda ya taimaki wani

Shaykh Ibnu Uthaimeen ya ce: Wanda ya taimaki wani a kan yi wa Allah da'a/biyayya cikin ayyukan da'a ma Allah, to yana da kwatankwacin ladansa ba tare da an rage wani abu daga nashi ladan ba".

Daga Sahl bn Sa'ad Yace:

"Manzon Allah (SAW) Yace: "Allah Yana da taskokin Alkhairi da na sharri, mutane su ne mabuɗansu, Madallah da bawan da ya zamo mabuɗin alkhairi makullin sharri, Tir da bawan da ya zamo mabuɗin sharri makullin Alkhairi".

Shaykhl Islam Ibn Taimiyyah (RA)

Ya ce: Misalin 'yan uwantaka saboda Allah, kamar misalin hannu da ido ne, idan ido ya zubar da hawaye sai hannu ya share masa, idan kuma hannu ya ji ciwo sai idon ya zub da hawaye sabo da zafin da hannu ya ke ji.

Allah

Subhanahu Wa taala- Yana cewa: وَلَا ‌تَقۡفُ مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٌۚ إِنَّ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡبَصَرَ وَٱلۡفُؤَادَ كُلُّ أُوْلَٰٓئِكَ كَانَ عَنۡهُ مَسۡـُٔولٗا ) [الإسراء: 36] Ma’ana: “Kuma kada ka bi abin da bã ka da ilmi game da shi. Lalle ne jĩ da gani da zũciya, dukan waɗancan (mutum) yã kasance daga gare shi wanda ake tambaya.”

Imam Azzahaby

yana cewa: "Idan Fitintinu suka afku, to ka yi riqo da Sunnah, Kuma ka kame bakin ka, kar da ka kutsa cikin abin da babu ruwan ka, duk abin da ya shige maka duhu to ka mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa(Me Allah da Manzonsa suka ce), ka tsaya(kar ka ce komai) ka ce: Allah ne Mafi Sani(Allahu a'lam)

Babu

:ani mai rubutu face sai ya gushe. Abin da kuma ya rubuta da hannunsa ya wanzu tsawan lokaci. Kada ka rubuta wani abu da tafin hannunka. Face abin da zai faranta maka rai ka ganshi ranar Alƙiyama.

Manzon Allah (SAW) Yace:

Babu wani Musulmi da zai yiwa ɗan uwan sa addu'a a bayan idon sa, face Mala'ika yace: Kaima Allah baka". (Muslim ya ruwaito)

Kyautatawa

*Kyautatawa* Ana bukatan mai Azumi ya yawaita kyauta ga talakawa da mabukata,

Nana Aisha (R.A)

Tana cewa: كان اجود الناس وكان اجود ما يكون في رمضان فلرسول الله صلى الله عليه وسلم اجود باالخير من الريح المرسلة Manzon Allah (SAW) yafi kowa karamci, kuma yafi karamci a cikin Watan Ramadan, kuma lallai Manzon Allah (SAW) yafi karamci da Alkhairi sama da iska mai ratsawa (ratsa jiki). [Bukhari da Musulim].

Samun nasara

HAKURI Haƙuri yana daga cikin abun da ya ke taya bawa samun nasara a duniya da lahira, duk abun da kuma aka ce babu haƙuri da juriya a cikinsa to zai wuya abun ya kai ga nasara.

Hakuri

Haske ne mai haskaka zuciya sai dai hasken tafe yake da zafi wanda sai bawa ya jure. Haƙuri ya fi dutse nauyi a zuciyar bawa kuma ya fi maɗaci ɗaci a zuciya sai dai amma ya fi zuma zaƙi da daɗaɗa rai wurin sakamako.

Hakuri

Imamu Ahmad yana cewa: “Haƙuri a cikin jikin ɗan Adam yana da matsayi kamar kai ne, kuma duk mutumin da ba shi da kai to gangar jikinsa ma ba tada amfani.”

إني أخاف الله رب العالمين.

Bawa mai haƙuri shine yake yin haƙuri akan dukkan abun da Allah Ya haramta masa. Wato koda na second ɗaya bawa baya bari zuciyarsa ta rinjaye shi. Shine wanda zai daure, ya cije, koda ya samu dukkan dama da ƙarfin aikata saɓon amma sai ya ce: إني أخاف الله رب العالمين. Wato ni ina tsoron Allah Ubangijin talikai.