HAKURI

Haƙuri yana daga cikin abun da ya ke taya bawa samun nasara a duniya da lahira, duk abun da kuma aka ce babu haƙuri da juriya a cikinsa to zai wuya abun ya kai ga nasara.

Shaykhul Islami Ibnu Taimiyyah (R)

"Mace tana da bukatar kula da tsaro sama da yanda karamin yaro yake da bukata, kuma duk abin da zai zamo ya suturce ta, ya katange ta, shi yafi gurin inganta mata rayuwarta."

Safiyanuth thauri (RahimahulLah)

"Babu abunda yafiwa Mace (alkhairi) kamar (zamanta acikin) gidan, ko da tsohuwace ita" Inji Safiyanuth thauri (RahimahulLah)

Manzon Allah (s.a.w)

"Mace bata kasancewa mafi kusanci ga Mahaliccinta (a wani wuri) fiye da acikin gidanta" [SilsilatusSahiha : 2688]

Imam Shaqidiy (R)

"Kasancewar mace ba ta fita daga gidanta (ba ta yawan fita) yana daga cikin sifofin kyawunta."

Alhaithamee

"Lalle fitan mace daga gidanta ta saka turare tayi kwalliya yana daga cikin manyan laifuka."

Ibnul Arabiy

"Mace Tagari ba tana zuwa bane da iya neman mutum, Ita arziki ne na Allah wanda yake bayarwa ga wanda yake tsoronshi."

Manzon Allah ﷺ

"Wanda Allah ya azurtashi da mace ta gari to hakika Allah ya taimakeshi a kan rabin addininsa, to ya ji tsoron Allah a sauran rabin". Shaykhul Islami Ibnu Taimiya(RA) ya ce: "Soyayya da rahama suna kasancewa daga wajenta, (Mace ta gari) abin da Allah ya yi mata baiwarsa "